[ANDROID User]
.
.

.KAR KAI WASA DA WANNAN POST DIN NAWA KA DAURE KA KARANTA DOMIN NASAN MATU QAR KANA RIKE WAYOYI ZAI AMFANI KA
.
.
.
MUHIMMANCIN GOOGLE ACCOUNT (GMAIL) GA MASU ANDROID PHONE
.

.
Tabbas nasan Duk wanda ya mallaki wayar Android, takan bukaci google account kafin ta fara aiwatar da komai na daga gareta.
.

.
Wanda wannan gmail account yana da muhimmanci ga masu wannan waya.
.

.
Domin kuwa GMAIL ACCOUNT Yana da sirrika da kuma amfani sosai

.
.
GA KADAN DAGA CIKIN AMFANIN DA GMAIL YAKE GA MASU RIKE WAYAR ANDROID
.
.

= Da gmail Account ne zaka i,ya dawo da duk kanin abinda ka goge ko ya fita misali wani matsala ya faru da wayar ka wanda wannan matsala takai ga har kayi ma wayar taka RESTORE, ko PLASHING to matuqar kana da wannan GMAIL din a wayar ka akwai hanyoyin da xaka bi ka dawo da komai cikin wayar ka.
.
.
= Da GMAIL ACCOUNT ne zaka i,ya bin diddigin wayar kada aka sace koda kuwa barawon ya cire sim card din ka ya jefar GMAIL account xai iya taimaka wa wajen ganin duk inda barawo yake | wannan hanyar munyi muku bayanin ta idan baku manta va ta yadda xaka bi diddigin wayar ka da aka sace ta wayar abokinka abinda

¤

¤
.
.
> Da GMAIL Account ne zaka iya kulle wayar ka da aka sace ta xamto barawon da ya sata wayar baxa tai masa amfanin komai ba | idan kuma kaga dama kayi FORMAT din wayar ta koda wayar tana hannun barawon da ya sata wayar ne
.
.

> Da wannan gmail account ne zaka samu damar sauko da applications, videos, photos da wakoki daga play store ko Market place na wannan waya.
.
.
> Da wannan gmail account ne zaka samu damar juya sauran applications din data zo dasu.

.
.
> Da wannan gmail account ne zaka bude wayarka Android, yayinda ta kulle, wato idan kasa ta acikin wannan key, sannan kuma wani yazo ya danna maka ba dai-dai ba, zata bukaci gmail account, to wannan wanda kasa mata shi take bukata.
> Rashin saka mata gmail account, zaisa kayi asarar wayarka yayinda ta shiga wannan hali na bukatar gmail account.
.

.
> karka manta password naka ka ajiyesu suna da muhimmanci agareka, karka dauka kamar ko dole ne akayi maka, tabbas ajiye tarihin wannan email naka, da password naka,
.

.
ka ajiyesu da kyau suna da rana.
> Abinda ake nufi da google account shi ne gmail account misalin google account
zeetown32@gmail.com
nafiukg@ gmail.com
nafiu3213@gmail.com
Wannan shi ne misalin Google account ko Gmail account, ko Gtalk account.
.
.

.
ME ZAI FARU IDAN KA MANTA GMAIL DA PASSWORD NAKA?
Idan kana amfani da Android phone, sannan kuma ka manta gmail naka, da password naka zai dawo idan ka san alternate email address naka. Rashin sanin wadannan abubuwa zai baka matsala akan wayanka, domin bazata dannu ba, babu wani abu da zatayi, naga amfani dole saika cire wannan google account da take bukata.
.

.
IDAN HAKA TA FARU ANA FLASHING?
Idan kana amfani da android sannan kuma ta tambayeka wannan code nata kasa, kuma ka manta shi,
.

.
to karkayi mata flashing domin yimata flashing bazai haifar da da mai ido ba, domin zaka rasa wasu abubuwa nadaga wannan wayan naka, domin wani applications din zasu fita kuma bazasu dawo ba,
.

.
sannan kuma zata samu matsala bangaren browsing nata.
.

.
HIKIMAR AMFANI DA GMAIL AKAN ANDROID
Kamfanin da suke yin android sun kwaikwayi, kamfanin Apple ne akan yadda suka tsara computar su da wayoyinsu, dansu gane mai wayar da wanda ba mai wayar ba, ta yadda da zarae ta shiga key,
.

.
to mai itane kadai zai iya budeta, inkuma ya kasa saidai aje kamfaninsu.
Amma akan samu matsala wajen sa wannan email, idan kasa ba dai-dai ba,
.

.
hartsawon sau goma ajere zasu gargadeka, da cewar ka tsaya haka, amma idan ka ci gaba har auwa 15, to imbakai wasa ba zatayi format na komai nata, nan take zata kashe kanta. Ta mutu kenan ko kuma kaje kamfaninsu dan samun mafita.
.

.
Masu saida wayar Android, kuna iya kokarinku wajen budewa duk wanda ya sayi wannan waya daga gareku, amma ku kara kokari, wajen fahimtar da mutum muhimmancin wannan gmail a wurinsa, da wayarsa. Sannan ku bashi bayanansa ya ajiyesu na email nasa, saboda faruwar matsala gaba.

.

.
Da fatan wannan dan bayani zai muku amfani
domin neman karin bayani sai ku neme ni ta [ 07065721492]

POSTED By... JABEER MC

Post a Comment

 
Top