TUNATARWA MAI DAUKE DA DARASI: Rayuwa Da Mutuwa

Daga Kabiru Zubairu Sheme

"Sun tafi sun kwanta a cikin kasa ba dan suna so ba, sai dan ajali ya yi kira kuma kwana ya kare, an yi ciwo an sha wahala rayuwa ta yi kunci daga karshe sun yi kwanciyar da babu tashi, haka kwanaki suke karewa akan mu, za mu yi ta tafiya har zuwa ranar da za a yi mana sallar da babu ruku'u balle sujuda, na yi zaton kwanaki za su rike mun amana, na yi zaton shekaru za su yi yawa a kaina, sai na ga sun kare mun a wannan rana.

Na yi burin abubuwa a rayuwa amma burin bai cika ba gashi ajali ya sauka a kai na, na yi burin na fadi wadansu maganganu ga masoya na amma numfashi ya yi tsada a yau, yau ni ne cikin makara na shigo a makare. Ya Rabbi ka yafe ni.

Da a ce na san Mala'ikun mutuwa suna hanyar zuwa gare ni da na bayyana password dina ga yan uwa na, bayan sun dawo gida daga rufe ni su rufe Facebook dina, in sun rufe ni su rufe WhatsApp dina.

Sai dai rai ya yi halin sa, makomar mu gun Allah, lallai na so a ce kafin raina ya fice na nemi yafiyar wadanda na bata musu, sai dai mutuwa ta sanya min ankwa, da a ce na san wannan shine ramin da za'a sanya ni da na koma zuwa ga Allah tun kafin yau da aka komar da ni zuwa ga Allah, lallai jiki ya yi nauyi, kwanaki sun juya zuwa tunanin ranar haihuwa ta.

Yau ce ranar da zan kwanta kwanciyar da Umma ta ba za ta iya tashi na ba, balle masoyiya ta, tashi na sai ranar tashin Shugaban Halittu Annabin da aka aiko zuwa gare ni (S.A.W), laifukan da nake yi na yi tunanin gyarawa da zuciya ta amma gabobi na sun ci amana ta, buri ya yaudare ni, na yi tunanin zan samu shekaru masu yawa sai gashi ajali ya sauka a kaina.

Tunani nake yi, yaya cikin gidan mu zai kasance idan za a fitar da gawa ta zuwa ga sallah? Zan zamo abin labari, za a rinka cewa a lokacin da wane yake raye kaza da kaza, amma fa a da nine nake labarin matattu, yau ni ne ake labari, na so na rike sallolin nafila da farillai akan lokaci, rayuwa ta rude ni, yau ni ne ake yi wa sallah, ni ne ake tunawa, kafin sati guda na san za su daina tunawa da ni.

Ya Allah Ka gafarta wa yayenmu, Malumammu, Sarakunmu, diya da jikokinmu, Ka nisantar da mu daga azabarKA, Ka gafarta mana, jikan mu da rahamarKA. Ka kare diyan mu daga sharrin zamani kafin mutuwar mu da bayan mutuwarmu, Ka nisantar da mu daga sharrin zamani.

Ya Allah! Ka bamu ikon taimakon addininKA, Ka sa mu yi amfani da rayuwar mu kafin mutuwarmu, kuruciyar mu kafin tsufan mu, lafiyar mu kafin rashin lafiyarmu. Amin.

Post a Comment

 
Top