KARANTA ABUBUWA 5 DA ZA SU HANA MASU NEMAN CIN MORIYAR SABON SHIRIN N-POWER SHIGA CIKIN SHIRIN.

Daga : Janaidu Amadu Doro.

1- Idan ka kasance ka na cikin sahun waɗanda su ke shirin N-Power na baya(Batch A and B), ko ka ƙara cike wa ba za ka yi nasarar kasancewa a sahun sababbin da za'a ɗauka ba.

2- Idan Nambar BVN ɗinka bai yi daidai da sunan da kayi rigistar N-Power ba, to ba za ka samu damar shiga sahun sababbin waɗanda za su ci gajiyar sabon shirin ba.

3- Idan ka yi kuskure wajan saka nambar asusunka(account number) ko BVN, to za a hanaka shiga sabon shirin N-Power.

4- Sannan idan ba ka yi nasara a gwajin da za'a gudanar a yanar gizo-gizo (online test) ba, duk da kasancewar  gwajin zai kasance mai sauƙi. A nan ma ba za ka samu nasarar shiga sabon shirin N-Power ba.

5- Idan ka yi kuskure a wajen zaɓar matakin karatunka ko ajin da ka ke , ba za ka yi nasarar shiga sabon shirin N-Power ba. misali mai NCE dole ya cike NTeach, mai Agric zai cike NAgro dasauransu.

Allah ya bai wa mai rabo sa'a.

Post a Comment

 
Top